Ibrahim Disina daya daga cikin fitattun Malaman addinin Musulunci a Najeriya ya wallafa a shafinsa na facebook cewar:
Yau Allah ya karbi ran shehin Malamin Islama, Marubucin littafin Minhajul Muslim, Dan gwgwarmaya Sheikh Abubakar Aljaza-iryy a kasar Saudiyya.
Shehu Malamin Dan shekara 98 ya dauki tsawon lokaci yana karantarwa a Masallacin Annabi SAW mai alfarma dake birnin Madina kai tsarki. Za a ayi masa sallah a Masallacin Manzon yau in sha Allah. Allah ya kyautata karshenmu.

LEAVE A REPLY