A gobe Laraba ne Firaministar Burtaniya Theresa May zata kawo ziyarar aiki zuwa Abuja babban birnin tarayyar Najeriya a wani rangadi da take yi na kasashen Afurka domin kulla yarjejeniyoyin kasuwanci.

May zata iso Najeriya ne daga kasar Afurka ta Kudu, inda zata gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sannan kuma zata ziyarci jihar Legas inda zata gana da gyauron mutanan da suka kubuta daga cinikin bayi.

Gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambide ne dai zai tarbi Firaministar yayin da ta Isa jihar Legas.

LEAVE A REPLY