Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan jihar Legas, Mista Akinwunmi Ambode sun sba wajen fadawa al’umma dalilin da ya sa Shugaba Buharin ya kai ziyarar aiki na kwanaki biyu a jihar Legas din.

Gwamnan Legas, Ambode ya bayyana a shafinsa na twitter cewa, Shugaba Buhari ya kai wancan ziyara ne don ya kaddamar da kafa harsashin birnin Eko Atlantic da gwamnatin jihar Legas ke ginawa bayan da ta tura ruwan teku ta samar da filin gina birnin.

Sai dai kuma mutane sun yi wa Gwamna Ambode caa a ka bayan da ya rubuta wannan sako a shafinsa, inda suka ci gaba da cewa ai Shugaba Goodluck Jonathan tare da tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton sun taba kaddamar da fara aikin a shekarar 2013 a karkashin mulkin tsohon gwamna, Babatunde Raji Fashola.

Fadar Shugaban kasa ta yi gaggawar sakin nata bayanin game da wannan batu don warware tinja-tinjar, inda ta rubuta a shafinta mai adireshi: @NGRPresident, cewa, “Shugaba Muhammadu Buhari ba kaddamar da aikin birnin Eko Atlantic ya je yi a Legas ba, ya dai ziyarci wajen aikin ne da tuni aka fara ya kuma yi nisa don ya ga yadda aikin ke tafiya.”

LEAVE A REPLY