Yusuf Buhari

Mai taimakawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan sabbin kafafan sadarwa na zamani, Lauretta Onochie ta karyata jita jitar da ake yadawa ta kafafan sadarwa na zamani cewar, Yusuf Buhari ya rasu.

Mataimakiyar Shugaban kasar ta bayyana a shafinta na Twitter cewa labarin rasuwar Yusuf Buhari ba shi da tushe balle maka. Ta kuma tabbatar da cewar Yusuf Buhari na nan cikin koshin lafiya.

Tun farko dai wani shafin yana gizo mai suna Nairaland ne suka fara kawo labarin cewar Yusuf Buhari ya rasu a ranar 20  ga watan Fabrairun nan. Lauretta ta kira labarin da cewar “Kanzon kurege” ta bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da wannan labarin.

Tuni dai shafin ya janye labarin daga kan turakarsa. Sannan dukkan rariyar likau din da aka yada ta labarin rasuwar Yusuf buhari ta dena budewa. Ya zuwa yanzu shafin na Nairaland bai yi wani karin bayani ba kan wannan labarin da ya bayar.

Idan ba’a manta ba, a ranar Talata 26 ga watan Disambar 2017, Yusuf Buhari ya gamu da wani mummunan hadarin babur a birnin tarayya Abuja, inda ya samu rauni a kwakwalwarsa, inda aka garzaya da shi asibitin Cadercrest dake Abuja don bashi kulawa.

Shafin jaridar DAILY NIGERIAN ne dai ya fara bayar da labarin hadarin da Yusuf Buhari yayi a wani wasan tseren babur da Yusuf din yake yi tare da wani abokinsa Bashir Gwandu, inda suka yi taho mu gama a yayin tseren.

Tun bayan da Yusuf Buhari yayi wannan hadarin bayanai suka tabbatar da cewar ya samu mummunan rauni a kwakwalwarsa, inda fadar Shugaban kasa a lokacin ta bayyana cewar Yusuf Buhari na samun sauki daga raunin da ya samu.

Tun bayan da yake kwance a asibitin yana karbar kulawa wasu majiyoyi suka bayyana cewar an fitar da Yusuf Buhari kasar Jamus domin cigaba da kula da shi a can. Tun da fadar Shugaban kasa ta bayyana cewar Yusuf Buhari ya samu sauki, ba’a kuma ganinsa a bainar jama’a ba har zuwa yanzu.

LEAVE A REPLY