Zahra Buhari

Daga Hassan Y.A. Malik

Fadar shugaban kasa ta nesanta kanta da wani shafin facebook mai dauke da sunan ‘yar shugaban kasa, Zahra Buhari.

A Faebook page with the name, Zahra Buhari recently featured a post with a picture of President Buhari walking on an airport runway in the snow.

Shafin mai dauke da sunan Zahra Buhari ya wallafa wani bayani mai dauke da hoton shugaban kasa Muhammadu Buhari na tafiya a wani filin tashin jirgi da dusar kankara ya rufe.

Shafin ya wallafa wannan hoto da bayani ne da tuni ya yadu a ranar 17 ga Afrilu ga kuma abinda bayanin ya ce:

“Bayin Allah, Wannan dattijo ne mai shekaru 75 ya ke tafiya a cikin dusr kankara ba tare da ya sanya rigar sanyi ba, kawai don ya ceto kasarsa daga matsalar tattalin arziki da ya addabi kasar, amma sai ga shi wasu ‘yan kasar marasa kan gado na dauka cewa dattijon na yin wannan tafiye-tafiye don jin dadin kansa.

Allah ya albarkaci Nijeriya!”

“Don Allah a yada…”

Sai dai fadar shugaban kasa ta nesanta kanta da wannan sako da ma shafin gaba daya.

Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya bayyana wanda ya bude shafin da suna Zahra Buhari, ta wata sanarwa da ya fitar,  a matsayin “Dillalin haddasa husuma.”

Ga sanarwar da Femi Adesina ya fitar:

“Wasu dillalan haddasa husuma a kokarinsu na ci gaba da shafawa iyalin shugaban kasa kashin kaji, sun bude wani shafin facebook mai dauke da sunan ‘yar shugaban kasa, Zahra Buhari.”

“Fadar shugaban kasa na nesanta kanta da wannan shafi da abinda ya wallafa a ranar 17 ga watan Afrilu da misalin karfe 9:07 na safe.”

“Fadar shugaban kasa har lau na jan hankalin al’umma da su yi burus da wannan bayani da ma shafin sakamakon mugun nufi da ke tattare da wadanda suka kirkiri shafin da ma sakon da suka wallafa.”

LEAVE A REPLY