Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Sarki Muhammadu VI na Moroko

Gwamnatin tarayyar Najeriya da masarautar kasar Moroko a ranar Litinin a babban birnin kasar Rabat, sun sanya hannu akan wasu yarjejeniyoyi guda uku wadan da ake sa ran dukkan kasashen biyu zasu ci gajiyarsu nan gaba kada,

Daga cikin yarjejeniyoyin da aka sanya hannu akansu sun kunshi batun nan na shimfida bututun iskar gaz da zai tashi daga yankin kudu maso kudancin Najeriya zuwa yankin kasashen Afurka ta yamma inda zai wuce har zuwa kasar Moroko daga nan kuma ya keta saharar kasar zuwa nahiyar Turai.

Shugaba Muhammadu Buhari tare da Sarki Muhammad na shida ne suka jagoranci wannan sanya hannu akan wadannan yarjejeniyoyi bayan da suka yi wata ganawa ta musamman a tsakaninsu a birnin Rabat na kasar ta Moroko.

Mai magana da yawun fadar Shugaban kasa malam garba Shehu shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya tabo batutun da aka sanyawa hannu tsakanin Najeriyar da kasar Moroko.

Batutuwan dai sun kunshi batun ayyukan gona da kuma ma’adanai. Shugaban hukumar gudanarwar babban kamfanin mai na kasa Farouk Said Garba shi ne ya jagoranci sanya hannu kan wannan yarjejeniyar a madadin Najeriya, yayinda Amina Benkhdra ta sanya hannu a madadin kasar Moroko.

Za dai a kammala wannan aikin shimfida bututun iskar gaz ne a cikin shekaru 25 masu zuwa, aikin da zai tuke har zuwa nahiyar Turai. Aikin shimfida wannan bututun zai ci tsawon kilo mita dubu biyar da dari shida da sittin (5,660km), wanda bayan kammala wannan aiki dubunnan ‘yan Najeriya ne zasu samu aikin yi ta sanadiyar shimfida wannan bututun iskar gaz.

LEAVE A REPLY