Daga Hassan Y.A. Malik

Bayan sakin sakamakon jarrabawar share fagen shiga jami’a da hukumar JAMB ta yi a makon da ya gabata, an sake samun wani yaro dan shekaru 17 da haihuwa da ya samu maki sama da na wanda ya ke da mafi yawan maki a sakin jarrabawa na farko da hukumar ta yi a bana.

Yaron da aka bayyana sunansa da Esan Ibunkunoluwa Caleb dan asalin jihar Ekiti ne kuma dan makarantar Shepherd International College ne ya samu maki 351

Esan ya rubuta English, Mathematis, Physics da Chemistry inda ya bugo wadannan makin: 78, 91, 97 da 85.

A terse statement by the school on Saturday shows that his JAMB number is 85346758FD.

Esan ya zana jarrabawarsa ta JAMB ne a cibiyar zana jarrabawar da ke jami’a mallakar jihar Ekiti.

Esan mai lambar jarrabawar JAMB kamar haka: 85346758FD ya zabi ya karanta Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa (Computer Science) a jami’a.

LEAVE A REPLY