Daga Hassan Y.A. Malik

A yau Talata ne shugaban kungiyar ‘yan uwa musulmi (Shi’a), Sheik Ibrahim El-zakzaky ya bayyana a gaban kotu a karon farko tun bayan tsare shi a watan Disambar shekarar 2015.

An gurfanar da shi a babbar kotun jihar Kaduna a cikin tsananin tsaro.

Idan mai karatu bai manta ba, an kama El-Zakzaky ne bayan wani rikici da ya barke tsakanin mambobi kungiyar shi’a da sojojin Nijeriya wanda ya haddasa rasuwar ‘yan shi’a sama da 340 da soja guda daya.

Game da kisan wannan soja ne ake tuhumar El-Zakzaky da laifin kisa da kuma wasu laifuka guda biyu da suka hada da taron jama’a ba bisa kai’da ba da hadin baki wajen aikata mummunan laifi.

An isa da El-Zakzaky da matarsa Zeenah kotun da misalin karfe 9:00 na safiyar yau.

Ba a bar ‘yan jarida ko wani wanda ba ma’aikacin kotun ya ketare titin da ya kai ga kotun ba, inda jami’an tsaro suka yi tsayin daka.

Lauyan El-Zakzaky, Maxwell Kyom ya bukaci kotu ta bada belin shi, inda kotu ita kuma ta bukaci a mika wannan bukata a rubuce.

Ba a iya ci gaba da sauraran karar ba saboda mutane biyu da ake tuhuma tare da El-Zakzaky ba su bayyana a gaban kotu ba.

An daga sauraran karar zuwa ranar 21 ga watan Yuni.

Biyo bayan wannan shari’a da aka fara, mambobin kungiyar shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna inda suka bukaci a saki shugaban na su.

 

LEAVE A REPLY