Itse Sagay SAN

Shugaban kwamitin da yake baiwa Shugaban kasa Shawara kan batun cin hanci da rashawa, Itse Sagay SAN a ranar laraba ya bayyana cewar abinda Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru el-Rufai yayi na rushe gidan Sanata abin ya wuce gona da iri.

Da yawan mutane ciki har da majalisar dattawa sun yi Allah wadai da matakin na Gwamna el-Rufai na rushe gidan Sanata Sulaiman Hunkuyi mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya.

Mista Sagay, ya shaidawa Indefendan cewar yayi matukar mamaki ganin el-Rufai, mutumin da yake matukar ganin girmansa, amma ya mayar da kansa tamkar dan tasha sabadi kawai sabanin Siyasa da ana iya magance shi, amma ya aikata wannan aikin assha.

A cewarsa, wannan danyan aikin da Gwamnan yayi zai iya sabbaba rusa zaman lafiyar siyasar jihar kaduna, duba da cewar tuni aka nada Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda zai sasanta ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da basa ga maciji da juna.

Wannan mummunar aika aikar da el-Rufai yayi, ko shakka babu tana iya shafar nasarar zaben Shugaba Muhammadu Buhari a 2019 a jihar Kaduna, dama jam’iyyar baki daya a fadin jihar ta Kaduna.

“Ina fada muku, lokacin da naga labarin yau da safe a labarai nayi matukar kaduwa ainun. A ganina, wannan tsabar zakewa ne da wuce gona da iri, domin el-Rufai mutum ne da nake ganin da mutunci da kima, amma ya zube warwas a wajena”

“Shi mutum ne da yake da son bin tsari da ka’ida, yana tsayawa kan maganganunsa, ban taba zaton zai yi irin wannan aika aikar ba, sabida kawai sabani na siyasa mutum yayi irin wannan danyen hukunci. Gaskiya na kadu, kuma bana farin ciki da abinda el-Rufai yayi”

“Gaskiya ya wuce gona da iri, wannan abin da yayi sam ba daidai bane, domin hakan zai janyowa jam’iyyar APC a jihar kaduna. Dole ne mutum yayi tunanin abinda zai je ya dawo, sam ban yi farinciki da wannan danyen hukuncin na Gwamna ba” A cewar Sagay.

 

LEAVE A REPLY