Senator Albert Bassey Akpan

Hukamar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta shigar da tuhuma a gaban babbar kotun tarayya dake Ekeja a jihar Legas, tana tuhumar Sanata Albert Akpan Bassey saboda ya karbi kyautar motoci 12 da kudinsu yakai Naira miliyan 254.

Shi dai sanatan mai shekaru 45 dake wakiltar Arewa maso gabashin jihar akwa-Ibom a majalisar dattawan Najeriya, an bayyana cewar ya karbi kyautar motocin ne daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2014 daga hannun wani dan kasuwa Olajide Omokore a lokacin da shi Bassey yake kwamishinan kudi a jihar Akwa-Ibom.

EFCC zata gabatar da tuhuma guda bakwai akan Sanata Bassey a gaban babbar kotun tarraya dake Legas kan zarginsa da cin hanci da rashawa, yayin da shima dan kasuwar da ya bayar da kyautarmotocin za’a tuhume shi da laifuka 14 da suke da alaka da bayar da cin hanci da rashawa ga ma’aikacin gwamnati.

 

LEAVE A REPLY