Malam Ibrahim Shekarau tare da Aminu Wali yau Laraba a harabar ofishin hukumar EFCC dake jihar Kano

Hukumar dake yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Minista Malam Ibrahim Shekarau tare da tsohon Minista Aminu Wali yau a harabar ofishinta.

Tun a jiya Talata ne dai hukumar ta gayyaci tsohon Gwamnan tare da Aminu Wali domin amsa tambayoyi kan batun kudin zabe, amma daga bisani ta sallame shi tace ya koma zata neme shi.

Sai dai kuma, a yau Laraba hukumar ta sake gayyatar Malam Shekarau tare da AMinu Wali inda ta tsare su a ofishinta, tun farkodai a yau dn sai da jami’an hukumar suka yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa dandazon magoya bayan Malam Shekarau da suka yi sansani a harabar hukumar.

LEAVE A REPLY