Tsohon Gwamnan jihar Oyo, Adebayo Alao-Akala
 

Hassan Y.A. Malik

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, reshen jihar Oyo, a yau Litinin ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar ta Oyo, Otunba Adebayo Christopher Alao-Akala a gaban babbar kotun jihar Oyo, da ke zamanta a Ibanda, bisa zargin yin sama da fadi da wuri na gugan wuri har Nairar Nijeriya biliyan 11.5.

Akala ya gurfana a gaban kotun ne tare da kwamishinansa na kananan hukumomi da al’amuran masarautu, Mista Hosea Agboola, da kuma wani dan kwangila kuma shugaban kamfanin Pentagon Consults, Mista Olufemi Babalola.

An gurfanar da su bisa zarginsu da laifuffuka 11 da suka hada da hada kai wajen bayar da kwangilar da bata cikin kasafin kudi, mallakar kadarori daga kudin da aka same su ta haramtacciyar hanya, boye ainahin mamallakin kadarori da dai sauran laifukan da aka same su da su.

Sai dai, wadanda a ke karar sun musanta zargin da a ke yi musu a gaban mai shari’a L.M. Owolabi.

Bisa kin amsa laifin da a ke zarginsu da shi ne ya sanya lauyan masu shigar da kara ya bukaci da a rike wadanda a ke zargi har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron karar, inda su kuma lauyoyi masu kare wadanda a ke zargi suka roki kotu da ta bar wadanda suke karewa da su ci gaba da cin gajiyar belin da aka basu a baya.

Mai shari’a Owolabi ya amsa rokon wadanda a ke zargi, inda ya amince da su je su ci gaba da zama a karkashin bali har zuwa ranar 6 ga watan Afirilu inda za a dawo kotu don ci gaba da sauraron karar.

LEAVE A REPLY