Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta karyata rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta na Twitter, inda aka bayyana cewar hukumar na hirin damke Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose.

A wata sanarwa da hukumar  ta fitara ranar Litinin, Kakakin hukumar, Wilson Uwujaren ya ce “Maganganun da ake yadawa a shafukan Twitter am basu yi kama da maganganun hukumar ta EFCC ba”.

Bayanan da aka yada a shafin Twitter na hukumar EFCC @officialEFCC a ranar Lahadi aka wallafa cewar hukumar na shirin damke Gwamnan na Ekiti kan wata badakalar Naira biliyan 1.3 da aka bankado.

Wannan bayanin na zuwa ne ‘yan awanni bayan hukumar  zabe ta kasa mai zamankanta ta bayyana sakamakon zaben Gwamnan jihar Ekiti.

Dan takarar Gwamnan Jam’iyyar PDP wanda Gwamnan Fayose yake marawa baya Kolafo Olusola-Eleka ya sha kaye a hannun Kayode Fayemi na jam’iyyar APC.

An dai wallafa cewar “Rigar kariyar da Gwamnan jihar Ekiti Peter Fayose yake da ita ta zo karshe, dan haka hukumar zata ayi duk mai yuwuwawajen damke shi tare da bincikarsa”

 

LEAVE A REPLY