Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanarda tsohon mataimakin Gwamnan jihar Bauchi Babayo Garba gamawa da tsohon Sakataren gwamnatin jihar da wasu mutum uku kan zargin badakala da kudin zabe da suka kai Naira miliyan 500.

Sauran wadan da hukumar ta gurfanar sun hada da tsohon sakataren gwamnatin jihar Hammayo Aminu da Ahmed Dandija da wasu karin mutum uku dukkaninsu ‘yan PDP a zargin da hukumar ke musu na karbar kudi miliyan 500 daga tsohuwar ministar mai Dizieni Allison Madueke.

A cewar hukumar mutanan da ake zargi sun karbi zunzurutun kudi Naira miliyan 500 daga hannun tsohuwar ministar domin sha’anin zabubbukan shekarar 2015 da ta gabata domin taimakawa jam’iyyar PDP samun nasarar zaben ta haramtacciyar hanya.

Wakilinmu ya ruwaito mana cewar dukkanin mutanan da hukumar take tuhuma sun bayyana a gaban kotun banda Ahmed Dandija da ba”a ga fuskar ba a yayin gurfanarda su a gaban kotu.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar a yayin zaman kotun, Alakin Mohammed Shitu ya saurari dukkan bangarorin guda biyu na wadan da ake kara da kuma bangaren hukumar EFCC, inda ya nemi a bashi awa biyu domin yayi tunin matakin da ya dace.

Sai dai kuma, bayan da alkalin ya dawo ya bayyana cewar tilas ne Ahmed Dandija ya bayyana a gaban kotu a ranar da za’a sake zama kafin alkali ya bayyana matsayarsa kan wadan da ake tuhuma.

LEAVE A REPLY