Ustaz Abdallah Umsan Umar

A yayin da yake gabatar da hudubar Sallar juma’a a Masallacin Juma’a na Usman Bin Affan dake kofar Gadankaya, Ustaz Abdallah Usman Umar yayi kira ga Musulmi da su bi koyarwar Manzon Allah sau dakafa.

Malamin yace bin umarnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a dukkanin koyarwarsa shi ne abinda dukkan Musulmi ya kamata ya tsaya akai ba tare da wasu kwana kwana ba.

A cewar malamin, duk wani abu da bai tabbata daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ba, to ba addini bane, haka kuma, ya umarci mutane da yawaita yin salati ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

Ya kara da cewar, manzom Allah da kansa ya koyarda ssalatin da za’a yi masa. “Duk wani salati da ba na manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ba, shirme ne a cewar malamin, kuma wanda duk ya karar da rayuwarsa wajen yin Salatin da ba na Manzon Allah ba ya shiga uku a ranar kiyama.

Malamin ya karkare hudubar da yin kira ga Musulmi da su tashi tsaye wajen nuna soyayya da kauna ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ta hanyar yin da’a da dukkanin koyarwarsa.

LEAVE A REPLY