A kokarinta na ganin an rage adadin mata marasa aure a hadaddiyar Daular ta Larabawa, ya sanya gwamnatin kasar ta kuduri aniyar ta ta tallafawa mazajen kasar da kudin kama gida domin samun sukunin auren mata ta biyu.

Ministan kula da gine gine da ayyuka na musamman Abdallah Belhaif Al-Nuaimi a hadaddiyar daular ta larabawa, shi ne ya bayar da wannan sanarwar a wani taron zartarwa na majalisar zartarwar kasar da ranar Laraba.

Related image

Ya bayyana cewar, a tsarin Sarkin kasar Sheikh Zayed na wadatar da al’ummar kasar wanda suka kara mata ta biyu da gidaje ya bayyana haka.

Related image

“Za’a samarwa da mata ta biyu gidan da yayi daidai da matar faroko take ciki” A cewar ministan.

Majalisar Ministocin kasar ta bayyana gamsuwarta da wannan shiri, a cewarta wannan shiri zai taimaka wajen rage adadin matan da ba su da aure a kasar.

https://i1.wp.com/fb.ru/misc/i/gallery/13198/832226.jpg?w=640

Related image

 

LEAVE A REPLY