Dubban jama'a a wajen Tijjani Ado Ahmad ranar Talata 24 ga watan Octoba, 2017.

A yau ne aka yi jana’izar sanannen dan jarida Tijjani Ado Ahmad wanda ya rasu kimanin sati uku da ya gabata a ƙasar Amurka yayin da ya je wata ziyarar aiki.

A kwanan baya dai ‘yan uwan marigayin su ka shaidawa wannan jarida cewa za’a kawo gawar mamacin ranar 8 ga wannan watan.

Sai dai kuma daga bisani dangin sun ce an samu jinkirin kawo gawar ne saboda cike wasu ƙa’idojin dauko gawa daga ƙasar Amurkan.

An dai yi jana’izar mamacin a Ƙofar Kudu ta Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, kuma dubban jama’a ciki har da mataimakin gwamnan jihar Kano da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi sun halacci yi masa Sallah.

Kafin rasuwarsa, marigayi Tijjani Ado Ahmad shi ke gabatar da shirin Turanci na ‘Greetings from America’ kuma yana daya daga cikin masu gabatar da shirin Barka da Hantsi a Gidan Rediyon Freedom.

Tijjani ya rasu yana da shekaru 39.

LEAVE A REPLY