Dubban jama’a ne suka fito zanga zangar nuna adawa da korar ma’aikata da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i yake yi a jihar. Mutanen sun yi fitar farin dango inda suke dauke da kwalaye da tutoci suna rera wakokin ‘yanci na kungiyar Kwadago ta kasa.

Tun da farko dai, sai da Gwamnatin jihar ta Kaduna ta gargadi ‘yan kungiyar ta Kwadago da cewar kada su kuskura su fito wannan zanga zangar, a cewar gwamnati ta hana dukkan wani taro na zanga zanga a jihar.

Da safiyar ranar Alhamis din nan, Gwamnatin ta jibge tarin jami’an tsaron da yawansu yakai 8,000 a sassan cikin birnin Kaduna, domin hana masu shirin yin zanga zangar fitowa. Amma duk da wannan barazana sai da Shugaban kungiyar Kwadago ta kasa Ayuba Wabba ya jagorancin dubban ‘yan kungiyar suka fito kan tituna suna nuna rashin gamsuwa da matakin Gwamna El-Rufa’i na korar ma’aikatan.

Shugaban kungiyar Ayuba Wabba, da ya jagoranci dubban jama’a zuwa gidan gwamnatin jihar Kaduna dake gidan Sa Kashim Ibrahim, yace babu wata barazana daga ko waye da zata iya hanasu fitowa domin bayyana da ra’ayinsu, tunda dokar kasa ta basu dama.

Shugaban kungiyar Kwadagon ya kuma zargin Gwamnan na jihar Kaduna da kin bin umarnin kotu tare da kokarin yin amfani da jami’an tsaro domin tarwatsa masu zanga zangar nuna adawa da abinda yayi na korar ma’aikata 36,000 a fadin jihar.

Mai taimakawa Gwamnan Kaduna akan sadarwa ne ya karbi kabukncin ‘yan zanga zangar a kofar gidan Gwamnatin, inda yace ya dau alkawarin mika sakonsu ga Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai da zarar Gwamnan ya dawo, tunda baya gari a yanzu.

LEAVE A REPLY