Shugaba Buhari tare da Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sallami Sakataren harkokin wajen AMurka, Rex Tillerson daga aiki, inda ya maye gurbinsa da daraktan gudanarwa na hukumar leken asirin AMurka ta CIA, Mike Pompeo, jaridar Washington Post ce ta ruwaito labarin.

Mista Tillerson dai yana Najeriya lokacin da aka bayar da wannan sanarwa, a wata ziyara da ya kawo a jiya Litinin. Tillerson ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari, kuma sun tattauna kan yadda za’a sako ‘yan matan Dapchi da aka sace.

Sanarwar sallamar Rex Tillerson daga aiki bata yi wani karin bayani na dalilin da ya sanya aka kore shi daga aikin ba.

LEAVE A REPLY