Shugaban rundunar soja ta Najeriya, Tukur Yusuf Buaratai ya kalubalanci rundunar sojan Najeriya da ta san duk yadda zata yi ta kamo Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram ABaubakar Shekau a mace ko a raye.

Mista Buratai ya bayar da wannan umarni na a kamo Shekau ne a lokacin da ya ziyarci inda ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka yi sansani a cikin dajin Sambisa inda rundunar sojan ta kira da ‘Camp Zero’ .

A shekarar 2017, Mista Buratai ya taba bayar da umarnin a kamo Abubakar Shekau cikin kwanaki 40, inda aka gaza kama shi. A yanzu dai rundunar sojan Najeriya ta sanya ladan Naira miliyan uku ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kame Shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau.

A shekarar 2016 rundunar sojan najeriya ta tabatarwatsa sansanin ‘yan Boko Haram dake cikin dajin Sambisa, inda daga bisani mayakan kungiyar suka kuma haduwa a cikin dajin suka sake kafa sansani,inda a wannan Shekarar aka kuma tarwatsa sansanin nasu.

Daga cikin gurare da Mista Buratai ya ziyarta sun hada da Bita da Tukumbere, dukkansu wasu gurare ne dake cikin dajin, amma ‘yan Boko Haram suka fatattaki mutanen da suke wajen suka kuma tarwatsa wajen.

“Ina muku murna da kuma fatan alheri. Amma ku sani sai mun shiga duk inda wannan matsiyacin yake domin kamo shi da ransa ko kuma a mace” A cewar Buratai.

“Shugaban kasa da kansa ya bani sako na gaya muku cewar, yana jinjina a gareku tare da yabawa kokarin na ganin kun kwato dajin Sambisa daga hannun ‘yan ta’addar Boko Haram”

NAN

 

LEAVE A REPLY