Shugaba Buhari tare da tsohon Gwamnan Abiya Orji Kalu

Tsohon Gwamnan jihar Abiya, Orji Kalu, a ranar Asabar ya yi kira na musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da uwara jam’iyyar APC ta kasa da su sanya baki kan rikicin da ya barke tsakanin Gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi da ministan sadarwa Adebayo Shittu.

Mista Kalu yayi wannankiran ne a birnin badun, lokacin da ake kaddamar da ofishin yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Osibanjo a zaben 2019 a yankin kudu maso yamma.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito Gwamna Ajimobi da masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar AC reshen jihar ta Oyo duk basu halarci taron ba.

NAN ta fahimci cewar, Gwamnan da jagororin jam’iyyar reshen jihar, suna Sakatariyar jam’iyyar dake Oke-Ado domin wani gangami a daidai lokacin da ake kaddamar da ofishin.

Mista Kalu ya bayyana cewar, da Gwamna Ajimobi da Minsita Shittu ya kamata ace sun zama aminan juna. ya cigaba da cewar, matukar ba’a dinke wannan baraka dake tsakanin mutanan biyu ba, to hakan na iya shafar nasarar jam’iyyar APC a jihar, a zaben 2019 dake tafe a shekara mai zuwa.

“Mu kam ba komai zamu yi ba, illa muyi kira ga wadannan mutane da su manta da dukkan bambancin dake tsakaninsu su zauna da juna lafiya. Mu kullum kiranmu shi ne a zauna lafiya, bamu da wani shayi dan bayyanawa mutane gaskiya ko da ba zata yi musu dadi ba”

“Duk wanda yake zaune a cikin dakin taron nan zai fahimci lallai, akwai wagegen gibi tsakanin Gwamna da Minista a wannan jihar, bama fatan hakan ya cigaba”

“Duk wanda yake nan wajen a tare da mu, kuma, ya bayyana gamsuwarsa da wannan halin da ake ciki na fadan manyan giwaye a jihar nan, to lallai ni da yayana Ken Nnamani ba zamu yadda da shi ba”

“Zamu yi dukka abinda zamu iya, wajen muga an shawo kan matsalar dake tsakanin manyan mutanen biyu, a sabida haka, muke kira ga Shugaban kasa da mataimakin SHugaban kasa, da jiga jigan jam’iyyar APC da su yi wani abu domin sasanta wannan rikici”

“Abu mafimuhimmanci a garemu shi ne mu fadawa juna gaskiya akan dukkan lamuran dake faruwa”

Haka kuma, tsohon Gwamnan, ya jinjinawa kungiyar yakin neman zaben Buhari da Osibanjo akan wannan taro da ta shirya, inda ya bayyana cewar Shugaba Buhari da mataimakinsa suna bukatar sake tsayawa zabe a karo na biyu.

A lokacin da suke tofa albarkacin bakinsu, Ministan sadarwa Adebayo Shitu da Ministan Lafiya, Issac Adewole sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su cigaba da marawa Shugaba Muhammadu Buhari baya domin samar da cigaba a kasarnan.

Shitttu yace, Gwamnatin Shugaba Buhari tayiwa kasarnan abin a zo a gani, ya kara da cewar, abinda Buhari ya cimma cikin Shekaru biyu, jam’iyyar PDP mai adawa bata iya cimma shi ba duk tsawon mulkinta.

“Zance na gaskiya shi ne, Shugaba Buhari yana yin iyakar kokarinsa, amma kadan ne cikin irin dumbin nasarorinsa ake bayyanawa mutane. Shugaba Buhari ya samar da aikin yi miliyan shida a cikin shekara biyu na mulkinsa, daga bangaren noma kawai” A cewarsa.

A nasa jawabin, Adewole, yace dole ne a jinjinawa Kalu da Nnamani a yunkurinsu na yin kira ga zaman lafiya da cigaban jam’iyyar APC a duk fadin Najeriya.

Ken Nnamani, shi ne Shugaban taron, a jawabinsa ya bayyana cewar, tilas jam’iyyar APC tayi abinda ya dace domin sasanta rikita rikitar cikin gida da ta mamaye jam’iyyar.

“Duk da yake cewar mun hadu a nan ne domin bude ofishin shiyyar kudu maso yamma na yakin neman zaben Shugaba Buhari, amma akwai yuwuwar samun dawwamammanezaman lafiya tsakanin ‘yan jam’iyyar APC”

NAN

LEAVE A REPLY