Kakakin majalisar wakilai ta kasa Yakubu Dogara

Kakakin majalisar dokokin na tarayya Rt. Hon. Yakubu Dogara ya taya Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki murnar samun nasara a kotun kolin tarayyar Najeriya, bisa zarginsa da kotun da’ar ma’aikata ta yi na kin bayyana kadarorin da ya mallaka a rakardun cikewa domin shiga zabe.

Dogara a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Turaki Hassan ya bayyana cewar wannan nasara da Bukola Saraki ya samu abin farinciki ne kwarai da gaske, ya kara da cewar wannan nasara ba ta Saraki kadai bace.

Ya karadacewar wannan hukunci ya kara sanyawa mutane kwarin guiwa akan tsarin Shariah na Najeriya. “Kuma wannan nasara ce ga demokaradiyyar Najeriya”

LEAVE A REPLY