Daga Hassan Y.A. Malik

Wani direba mai shekara 18 ya bayyana a gaban kuliya a bisa zargin sa da ake yi da yi wa wata ‘yar shekaru 14 fyade.

Saurayin mai suna Msughter Agadoon dan yankin Wurukum ne a Makurdi, babban birnin jahar Benue.

Kotun majistare da ke Makurdi inda aka gurfanar da shi ana tuhumar sa da laifukan da suka hada da hadin baki da kuma fyade.

Dan sanda mai kara Micheal Iorondu, ya shaidawa kotun yadda wata Margaret Ezekiel ta kawo rahoton faruwar lamarin ranar 20 ga watan Maris.

Ya ce, Ezekiel ta ce ta tura yarinyar ne don ta je mata aika, sai wanda ake zargin tare da wani dake tafe da shi suka ja ta suka yi mata fyade a cikin wani kango.

“Mun samu damar kama Agadoon, amma dayan ya tsere,” inji Iorondu.

Yanzu dai an daga sauraren karar zuwa ranar 19 ga watan Yuni, tare da bada umurnin mayar da wanda ake zargin gidan kaso kafin a yanke masa hukunci.

LEAVE A REPLY