Dino Melaye, yayin da ya fado daga motar 'yan sanda

Daga Hassan Y.A. Malik

Sanata mai wakiltar mazabar Bayelsa ta gabas, Sanata Ben Bruce a yau Litinin ya bayyana dalilin da ya sanya sanata Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya yi kuli-kulin kubura ya dirgo daga motar ‘yan sanda tana cikin tafiya a Abuja.

Melaye a makon da ya gabata ya tsirgo daga kan motar ‘yan sanda a sa’in tana cikin tafiya za ta kai shi jiharsa ta Kogi don amsa wasu tuhume-tuhume da ake yi masa na manyan laifuka.

 Lamarin ya yi sanadiyyar samun raunakan a jikin Dino dalilin da ya sanya aka kwantar da shi a sashen bayar da agajin lafiya na gaggawa na babban asibitin tarayya na Abuja.

Sanata Ben Bruce ya bayyana dalilin da ya sanya Melaye ya yi tsalle ya dirgo daga motar ‘yan sandan tana cikin tafiya.

“Sanata Melaye na fama da cutar asma, amma duk da haka bai sa ‘yan sanda sun ki fesa masa barkonon tsohuwa ba, wannan ya sanya dole ya tsirgo daga motar tasu don ya tserar da ransa.”

Sanata Ben Bruce ya bayyana ta shafinsa na twitter cewa dirowar da Melaye ya yi daga motar ‘yan sanda gudun ceton rai ne.

Ben Bruce ya rubuta: Yanzu na gana da @dino_melaye. Abin takaici ne jin abun da ya faru da shi. Dino na da cutar asma, amma sai ga shi ‘yan sanda sun fesa masa barkonon tsohuwa akan hanyarsu ta kai shi jihar Kogi, dalilin da ya sanya ya yi ta fama da numfashi. Da suka sake fesa masa barkonon sohuwar a karo na biyu ne ya sanya dole ya yi tsalle ya dirgo daga motar. Dino ya yi gudun tsirar da rayuwarsa ne daga hannun ‘yan sanda. Abin takaici!

 

 

LEAVE A REPLY