Mataimakin Shugaban jami’ar Bayero dake Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Belloa ranar Litinin ya bayyana cewar Digirin girmamawa da jami’ar take bayarwa ba na sayarwa bane, sai wadan da suka cancanta ne zasu samu.

Farfesa Yahuza Bello yana magana ne domin mayar da martani ga masu cewar wasu mutane na tururuwarzuwa jami’ar domin su bada baki a basu digirin girmamawa, yayi wannan jawabi ne a shirye shiryen da ake na bikin yaye daliban jami’arda suka samu nasarar kammalawa.

A cewarsa, majalisardattijai ta jami’ar da kuma majalisarzartarwa ta jami’ar sune suke zaunawa su fitarda sunayen mutanan da suka dace a basu digirin na girmamawa, dan haka yace, a wannan lokacn da za’a yi bikin yaye dalibai babu wanda jami’ar zata karrama da digirin girmamawa.

A tsarin dokarjami’arshi ne duk mutumin da ya nemi a bashi digirin girmamawa to fa ya barar da damarsa ko da kuwa ya cancanta matukar shi ne da kansa ya nemi a bashi.

Mataimakin Shugaban jami’ar ya karada cewar a bana jami’ar Bayero zata yaye dalibai 8,634 a fannoni daban daban, akwai dalibai 72 da suka samu daraja ta daya a karatunsu, sannan akwai 5,401 da suka ci nasarar kammala digirin farko, sai kuma dalibai 1,833 da suka samu nasarara kammala digiri na biyu, sannan kuma mutane 70 suka ci nasarar kammala karatu a matakin digiri na uku wato PhD; sannan kuma sai dalibai 656 da suka ci nasarar kammala karatun babbar diploma.

Za dai a gudanarda bikin yaye daliban ne a ranakun 3 ga watan Afrilu zuwa 7 ga watan na Afrilu, sannan za’a gabatar da mukala mai take “Shugabanci, tsaro, Demokaradiyya da kuma kalubalen dake tattare da cigaban nahiyar Afurka” Manyan masana ne da jakadu zasu gabatar da wannan tattaunawa.

LEAVE A REPLY