Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewar nan da wani lokaci kankani batn dauke wutar lantarki a Najeriya zai zama tarihi, domin Gwamnatin tarayya tana yin iyakar yinta wajen gannin ta wadata Najeriya da hasken wutar lantarki da ‘yan kasarsuke bukata.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a yayin da ya jagoranci wani taron tattaunawa da al’umma da ya gudana a birnin Badun na jihar Oyo.

Ofishin mataimakin Shugaban kasa da hadin guiwar Gwamnatin jihar Oyo ne suka shirya wannan taron da ya gudana a babban dakin taro na Ogunlesi dake babban birnin jihar Badun.

Osibanjo yace aikin da Gwamnatin tarayya ta yi zai baiwa manyan manyan kamfanonin rarraba wwutar lantarki damar zuwa su sanya jarinsu domin rarraba wutar ga masu bukata a dukkan fadin Najeriya.

 

LEAVE A REPLY