Knar Sambo Dasuki mai ritaya

Tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro kanar Sambo Dasuki ya isa babbar kotun daukaka kara ta Gwamnatin tarayya domin ya bayar da shaida akan shariar da ake yiwa tsohon kakakin jam’iyyar PDP na kasa Olisa Metuh.

Tun farko, babbar kotun daukaka kara ce ta bukaci hukumar tsaron farin kaya ta kasa SSS da ta gabatar da Kanar Sambo Dasuki domin ya bayar da shaida kan shariar da ake yiwa Olisa Metuh.

Kanar Sambo Dasuki dai yana tsare a hannun hukumar tsaron farin kaya ta SSS tun fiye dda shekara guda, ana zarginsa ne da yin almubazzaranci da kuma sama da fadi da facaka miliyoyin nairori.

LEAVE A REPLY