Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu

Wani babbana darakta a hukumar EFCC, Ayo Olowonihi ya maka mukaddashin Shugaban hukumar Ibrahim Magu a kotu sabida rage masa mukami da akai ba bisa ka’ida ba wanda shugaban hukumar yayi.

Mai shigar da karar ya maka Magu a kotun a takardar da ya aikewa kotun mai lamba NICN/ABJ/347/2017 inda yake karar Magu da cewar ya rage masa muka ba bisa doka ba, yake rokon kotu da ta rushe wannan hukunci da Magu yayi na rage masa mukami.

Lauya mai kare wanda yake kara J.O Amupitan, SAN ya shaidawa alkalin kotun Sanusi Kadu dake Abuja cewar wanda yake karewa an nada shi mai lura da sashin horas da ma’aikata da suke matakin albashi na 16 a shekarar 2005, daga bisani kuma aka mayar da shi kwamandan EFCC a maris din 2012.

Yace, Mista Olowonihi ya bayyana cewar bayan ya zauna jarabawar karin girma kuma yaci, an kara matsayi zuwa kwamanda mai lura da wani aiki na musamman a watan Agustan 2013.

Ya zargi cewar, Magu a 19 ga watan Nuwamban 2015, ya bukace shi cikin gaggawa, inda ya zargeshi da hannu kan wasu bayanai da aka wallafa a shafukan sadar da zumunta na yanar gizo, wanda suka shafi mutuncin shi Magu din.

Yace umarnin da Mista Magu ya bayar, an shaida masa cewar an karbe wata kwamfutar tafi da gidanka ta shi daraktan hukumar, sannan aka karbe wayoyinsa guda biyu, sannan aka yiwa ofishinsa binciken kwakwaf daga wasu jami’ai na musamman da suka kunshi ‘yan sanda, kana daga bisani aka rufe masa ofis.

Yace duk da haka Magu bai daddara ba sai da ya rage masa matsayi a hukumar, inda ya mayar da shi makarantar horarwa ta hukumar.

A cewarsa wadannan abubuwan anyisu ba bisa doka ba, a sabida haka yake rokon kotu da ta tursasa Magu ya mayar da shi kan mukaminsa da aka rage masa.

LEAVE A REPLY