Kamfanin Dangote ya fara aikin gina titin da aka yi da Siminti mafi tsawo daga Obajana zuwa Kabba a yankin jihar Kogi.

Babban manajan daraktan kamfanin mai lura da sashin gine gine, Ashif Juma, shi ne ya bayyana hakan a Lakwaja a ranar Litinin, inda yace za’a kammala aikin kamar yadda aka tsara shi.

Ashif Juma yace, ya zuwa yanzu anci kimanin kilomita 33, kuma yace kilomita 23 duk titin siminti ne, yace aiki ne mai kwari da inganci, kuma ana sa ran kammala shi nan da zuwa watan Disambar nan mai zuwa.

A cewarsa, hanyar Objana zuwa Kabba tana da tsawon kilomita 44, yace ita ce aikin titi mafi tsawo na siminti da aka taba yi a Najeriya, ya kara da cewar, ita ce hanyar da zata sadar da yankin kudancin kasarnan da kuma Arewa.

 

LEAVE A REPLY