Adebo Ogundoyin

Wani matashi mai Adebo Ogundoyin ya lashe zaben cike gurbi na kujerar dan majalisar dokokin jihar Oyo mai wakiltar Ibrarafa ta gabas.

Matashin ya kammala karatun digirin farko a jami’ar Babcock.

Ogundoyin ya lashe zaben nasa ne da kuri’u 6,277 inda ya kayar da abokin karawarsa dan jam’iyyar APC mai mulkin jihar Olukunle Adeyemo inda kuri’u 4,619.

Wannan zaben cike gurbi dai ya biyo bayan mutuwar dan majalisar dokokin yankin da ya rasu a kwanakin baya.

LEAVE A REPLY