Daga Hassan Y.A. Malik

Asirin wani dan sanda da aka bayyana sunansa da Henry da ke aiki da ofishin ‘yan sanda na dibishin din Ojo da ke jihar Legas, bayan da ‘yar wata yarinya mai shekaru 16 da haihuwa da dan sanda Henry ya sace, ya yi ta kuma aikata fydae akanta, lamarin da har ya sa yarinyar ta samu juna biyu.

Iyalin yarinyar da ba a bayyana sunanta ba ne suka rubuta takardar kukansu zuwa ga sufetan ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Kpotun Idris.

Takardar ta bayyana yadda wannan dan sanda ya matsantawa yarinyar mai shekaru 16  da ‘yan uwanta bayan ta haihuwa wata biyar da suka wuce, dalilin da ya sanya dole ‘yan uwanta suka turata ta koma kauyensu da zama a jihar Anambra.

A yayin da yayar yarinyar mai suna Chukwudumaga Obadike ta ce: “A ranar 8 ga watan Mayun 2017 ne na nemi kanwata mai shekaru 16 da haihuwa na rasa, a saboda haka ban yi kasa a gwiwa ba na kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Ajangbadi a jihar  Legas.

“Watanni biyu bayan na kai wannan rahoto, a ranar 10 ga watan Yuli ne sai ‘yan sandan dibishin din Ojo suka zo suka tafi da ni bisa laifin wai ‘yar uwarta (da ta bata) ta saci kudi Naira miliyan 1.5 na wani jami’insu mai suna Henry.

“Bayan mun isa ofishin ‘yan sanda na Ojo ne na fada wa ‘yan sanda tsawon lokacin da na dauka ina nemanta kuma har na yi rohoto ga ofishin ‘yan sanda na Ajangbadi. ‘Yan sandan dibishin din Ojo suka dauke ni suka rankaya da ni ofishin ‘yan sanda na Ajangbadi don tabbatar da gaskiyar lamarin.

“‘Yan sandan ofishin dibishin din Ojo sun so su tsare ni amma na ki yarda, daga baya dai suka sallame ni da misalin karfe 11:00 na dare tare da umarta da na kawo kaina kashegari.

Chukwudumaga ta ce, daga baya dai mun samu kanwata a kauye sannan muka dawo da ita Legas don bada nata labarin na abinda ya faru, inda ta bayyana yadda dan sanda Henry ya tare ta a ranar da ta bata ya kuma sunkuceta ya yi otal da ita ya kuma ta yi mata fyade babu kakkautawa.

Daga baya dan sanda Henry ya dauki yarinyar ya kaita gidansa ya kuma dankata a hannun mai dakinsa a matsayin ‘yar aikin gida, kuma ya ci gaba da yin lalata da ita a duk lokacin da matarsa bata gida.”

Jaridar Vanguard ta tuntubi kwamanda ‘yan sanda yaki da fashi da makami SARS na Ikeja, jihar Legas mai suna Muhammad Sanusi, wanda ya karyata faruwar lamarin da cewa, ba a taba tsare wani mutum mai karancin shekaru a karkashin jagorancinsa ba.

“Bana yarda da tsare yara wadanda shekarunsu bai kai 18 a magarkamarmu ta SARS. Watakila suna yin haka kafin na zo, amma tun da na zo ba a taba tsare karamin yaro ba.”

LEAVE A REPLY