Wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane bakwai a yau lokacin da suka je masallaci domin Sallar Asubah a yankin karamar hukumar Konduga dake jihar Borno.

Shugaban kungiyar ‘yan sintirinyankin ALi Kolo shi ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya aukuwar lamarin.

Ali Kolo ya kara da cewar, akwai karin mutane bakwai da suka samu munanan raunuka ciki har  da wani karamin yaro a lokacin da dan kunar bakin waken ya tayar da bom din da ke jikinsa.

Dan kunar bakin waken dai ya ci nasarar kunna kai cikin masallacin dake yankin unguwar Mainari a karamar hukumar Kunduga inda ya kaddamar da harin.

Shugaban hukumar bayar  da agajin gaggawa ta jihar Borno, Bello Danbatta ya tabbatar da faruwar wannan al’amari. Yace tuni aka garzaya da wadan da suka ji raunuka asibiti domin karbar Magani.

LEAVE A REPLY