Daga Hassan Y.A. Malik

Wani mutum mai shekara 29 ya shiga hannun hukuma bisa zargin shi da ake da yi wa yarinya ‘yar shekara 13 fyade a jihar Ogun.

Mutumin mai suna Soji Ogunrinola wanda aka fi sani da buldoza (bulldozer), ya aikata wannan laifi ne a kauyen Ogiri Ojule da ke karamar hukumar Odeda a jahar.

Yayin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun ‘yan sandan jahar, Abimbola Oyeyemi ya ce sun cafke mutumin ne bayan da suka samu korafi akan shi daga gurin mahaifin yarinyar.

Mahaifin ya shaida wa ‘yan sanda cewa sai da mutumin ya yi barazanar kashe yarinyar idan har ta sake ta tona masa asiri.

Mahaifiyar yarinyar dai ita ta gano faruwar lamarin bayan da ta ga tabbare-tabbaren jini a jikin yarinyar.

Da ta tambayeta, yarinyar ba ta boye mata komai ba.

“Mahaifiyar, wacce dama ta san mutumin dan daba ne a kauyen, ta fada wa mijinta, sannan shi kuma ya kai rahoto wajen ‘yan sanda,” inji Oyeyemi.

Yayin da aka kama mutumin, ita kuma yarinyar an kaita asibiti domin a duba lafiyar ta.

LEAVE A REPLY