Sanata Dino Melaye

Daga Hassan Y.A. Malik

Lauya mai kare Sanata Dino Melaye, Mike Ozekhome ya magantu kan shari’ar wanda ya ke karewa a gaban kotu.

Dino Melaye ya gurfana a gaban kotu a yau Alhamis bisa zargin samunsa da hannu dumu-dumu wajen aikata mugun laifi, dalilin da ya sanya kotu ta bayar da umarnin ya ci gaba da zama a karkashi kulawar ‘yan sanda har zuwa ranar 11 ga watan Yuni.

Ozekhome, wanda lauya ne mai matsayin SAN ya fadawa jaridar Premium Times cewa hukuncin kotu na barin Dino a karkashin kulawar ‘yan sanda na da nasaba da baiwa sufeto janar din ‘yan sanda ya ci gaba da bawa Dino kulawa da kariya.

“Mai shigar da kara ya nemi kotu da ta tsare Dino a gidan yari, amma sai mai shari’a ya ki amincewa da bukatar mai shigar da karar, inda ya damka tsaro da kulawar Dino a hannun sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya har zuwa lokacin da Dino din zai warware 100 bisa 100.

“Wannan na nufin ‘yan sanda basu da zabi illa su mayar da Dino babban asibitin kasa na Abuja tunda dai asibitocin jihar Kogi na yajin aiki.”

Har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto, babu tabbacin ko dai ‘yan sanda za su dawo da Dino Abuja ko kuma za su bar shi a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

LEAVE A REPLY