Shugaba Buhari tare da Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson

Daga Hassan AbdulMalik

Awanni 12 kacal bayan da Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson ya kawo ziyar aiki Nijeriya ya kuma gana da shugaba Muhammadu Buhari, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana sallamar Rex din daga aiki a shafinsa na twitter.

Bisa dalilin da yasa aka salli Tillerson daga mukaminsa kuwa, Shugaba trump ya bayyana cewa, Sakataren harkokin waje, Tillerson ya kausasa harshe ga Shugaba kasar Rasha, Vladimir Putin duk kuwa da jan kunnen da Trump ya yi wa masu rike da mukaman gwamnati da kar wanda ya kuskura ya fadi wata magana ta tunziri ko kausasawa ga Putin da kasar Rasha bisa kowane irin dalili.

“Yanzun nan na kori sakataren harkokin waje, Rex Tillerson daga aiki. Jiya Rex ya kausasa harshe ga Putin.”

“Na gargadi dukkan ‘yan Amurka da kada su yarda su kalubalanci Putin ko Rasha koda kuwa sun aikata abubuwan da a zahiri suke nuna suna yakarmu. Mike Pompeo zai karbi aikin Rex.” Shugaba Trump ya rubuta a shafinsa na twitter.

A jiya Litinin ne dai Shugaba Muhammadu buhari ya karbi bakuncin Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson.

Bayan ganawar tasu ne, Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yanke hukuncin tattaunawa da mayakan Boko Haram a matsayin hanyar ceton ‘yan matan Dapchi da aka sace

LEAVE A REPLY