Daga Hassan Y.A. Malik

Wata matar aure da aka bayyana sunanta da Fatima Adamu mai kimanin shekaru 15 da haihuwa ta shiga hannun jami’an ‘yan sandan jihar Neja bisa zarginta da laifin kashe ‘yar kishiyarta mai shekaru 5 mai suna Hauwa

Rahotanni sun bayyana cewa Fatima ta yi nasarar kashe Hauwa ne da taimakon tsohon saurayinta mai suna Usman Muhammad a hanyar ciyar da ita da guba.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, Fatima da Usman sun jefar da gawar Hauwa a wani daji da ke kusa da unguwarsu, kuma an samu gawar ba tare da wasu bangarori na jikin Hauwa ba.

Wannan lamari dai ya faru ne a kauyen Egbati da ke karamar hukumar Agaie a jihar ta Neja.

A yayin da ‘yan sanda ke gudanar da tuhuma akan Fatima, ta tabbatar da cewa ita ta aikata kisan ta hanyar ciyar da yarinyar da gubar da tsohon saurayinta mai suna Usman ya hada mata.

“Da gangan na kashe ‘yar kishiyar tawa saboda na ki jininta, a duk lokacin da na ganta sai na ji tsanarta a raina. Wannan ya sanya na nemi yadda zan ga bayanta ta hanyar ciyar da ita da guba.

“Ina matukar takaicin aikata wannan abu da na aikata ga yarinyar da bata ji ba bata gani ba kuma bata yi min wani laifi ba. Ina fatan Allah ya yafe min bisa wannan aika-aika da na yi.”

Shi ma Usman Muhammad ya tabbatar da taimakawa wajen kashe Hauwa inda ya ce “Na gurbata rayuwata Ni na hada gubar da aka ciyar da yarinyar da bata ji ba bata gani ba. Na yi nadamar abinda na aikata.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Abubakar Muhammad. ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike za su gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

LEAVE A REPLY