Jarumar finfinan Hausa, Rahama Sadau

Darakta Janar na hukumar tace finafinai ta jihar Kano, Ismaila Afakallah ya bayyana dalilin hukumarsa na sahalewa jarumar finafinai Rahama Sadau dawowa ta cigaba da yin fim a masana’antar finfinai ta Kannywood.

Tun farko dai kungiyar masu shirya fin da wakoki ta MOPPAN ce ta bayar da sanarwar korar Rahama Sadau daga shiga cikin harkar fim a masana’antar sabida wani faifan bidiyo da ta fito tana runguar wani mawaki.

Ita kungiyar MOPPAN bata bayar da wani dalili na dawo da Rahama Sadau harkar fim ba. Amma da yake zantawa da sashin Hausa na BBC, daraktan MOPPAN ya bayyana cewar, tunda Rahama Sadau ta yi nadamar abinda ta aikata wannan kadai ya isa ya sa su yafe mata.

“Tun farko Rahama Sadau ta nemi afuwar mai martaba Sarkin Kano a matsayinsa na uba a jihar Kano. Sannan kuma ta nemi afuwar Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma sauran abokan aikinta na industiri”

“A rayuwa kowa yana iya yin kuskure, kuma ko a Musulunci idan mutum yayi kuskure kuma yayi nadama, to ya dace ace an yafe masa ankuma karbi afuwarsa”

“Wannan shi ne dalilin da ya sanya, hukumar ace finfinai ta jihar Kano ta gamsuwa da nadamarta kuma ta yafe mata”

“Tunda taui nadama kuma ta nemi afuwa, mun karbi nadamarta da afuwar da ta nema an bata, sannan zamu cigaba da duba finafinanta a masana’antar shirya fim tare da tace su” Inji Afakallah.

 

LEAVE A REPLY