Nuhu Gidado

Daga Hassan Y.A. Malik

Dalilai sun bayyana na abinda ya sanya mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Nuhu Gidado ya bayyana yin murabus daga kujerarsa a jiya Laraba.
Alhaji Nuhu Gidado ya mika takardar ajiye aiki ne a jiya Laraba, kuma tuni hadimansa suka shaidawa manema labarai labarin ajiye aikin maigidan nasu.

Takardar ajiye aikin na mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya isa ofishin sakataren gwamnatin jihar ne ta hannun mataimaki na musamman ga mataimakin gwamnan kan harkokin yada labarai, Yakubu Adamu.

A takardar, Alhaji Nuhu Gidado ya bayyana dalilansa na yin murabus da suka hada da alkawari da ya yi tun da fari na cewa zai rike wannan mukami na wa’adi daya tal wato shekara 4 kenan.

Mataimakin gwamnan, a takardarsa ya ci gaba da cewa, “A ka’ida kamata ya yi na ci gaba da rike mukamina har zuwa karshen wa’adinmu na farko da zai kama daidai da ranar 29 ga watan Mayu, 2019, amma bisa dalilin na samu kaina a wani yanayi na kwalewar gwiwata da rashin karsashi sakamakon yadda abubuwa ke gudana a siyasar jiharmu da kuma yanayin aikina, ya sanya na ga ya zama wajibi na ajiye aiki don tabbatar da adalci ga kujerar da na ke rike da ita da kuma adalci ga jiharmu da kuma kai mai girma gwamna a matsayinka na shugaba kuma dan uwa.

“Na tabbata za ka tuna ko a ranar Alhamis, 19 ga watan Afrilu, 2018 sai da na yi maka batun yin murabus dina a wata tattaunawa da mu ka yi ni da kai a ofishinka ya mai girma gwamna.

“Ina mai takaicin bayyana maka cewa na zabi bin abinda zuciyata ta fada mini game da ajiye aikina, kuma ina fata hakan ya zama shi ne mafi alkhairi a gareni da kai da ma al’ummar jiharmu baki daya.”

Shi ma wani dan uwa na jini ga mataimakin gwamnan kuma mataimakinsa na musamman kan harkokin cikin gida, Safiyanu Gidado ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai NAN wannan labari a jiya Laraba ta wayar tarho.

LEAVE A REPLY