Wasu dalibai yan Najeriya su 12 zasu fukanci fushin kuliya a kasar Benin sakamakon yin damfara ta hanyar Intanet.

Mai taimakawa Shugaban kasa ta musamman akan ‘yan Najeriya dake kasashen waje, Abike Dabiri ce ta bayyana hakan, inda tace tuni aka bayar da belin bakwai daga cikin 12 da ake tsare da su.

An bayyana sunayen daliban kamar haka Mathew Langgapp da Bayo Oyegunga da Tari Bori da Samuel Akinwande da Daunchi Dennis da Steven Porobunu da Chukwudi Valentine da Peter Ochani da David Esu da Emmanuel Chukwuneke da Timi Ogunleye da kuma Jacob Oluwatobi.

Madam Abke Dabiri ta kara da cewar jakadan Najeriya dake kasar ta Benin Kayode Oguntuase ne ya sanar da su halin da daliban suke ciki a kasar.

Jami’an tsaron kasar ne dai suka dinga bibiyar sawun daliban da suke mu’amala da Intanet wajen aikata damfara da zamba cikin aminci har suka gano su kuma suka yi awon gaba da su.

 

LEAVE A REPLY