Daliban kwalejin Ilimi ta tarayya dake Panshin sun fuskaci fushin Shariah,inda Alkalin Babbar kotun jiha dake da mazauni a Kasuwan Nama a birnin Jos ta tasa keyar daliban zuwa zaman gidan kaso na shekaru biyu sakamakon mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Mai Shariah Yahaya Mohammed, ya daure Pnret Jacob dan shekaru 22 da Peter Wunying dan shekaru 24 daurin wata shida a gidan yari kowannensu saboda hadin baki dan aikata laifi, tare kuma da daurin shekara biyu kowannensu ko kuma zabin biyan tarar Naira 20,000 kowannensu.

Alkalin kotun ya bayyana cewar yana fatan wannan hukunci ya zama darasi ga sauran al’umma da suke da tunanin daukar makamai domin tayar  da hankalin al’umma ko aikata ayyukan ta’adsanci.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar mutanan sun amsa dukkan laifukan biyu da ake cajinsu akai, a saboda haka suka samu afuwar kotu aka yi musu rangwamen hukunci.

 

LEAVE A REPLY