Gwamnan jihar Adamawa, Bindow Jibrila

Karamar hukumar Fufore dake jihar Adamawa ta baiwa dalibai ‘yan asalin yankin karamar hukumar su 100 dake karatu a manyan makarantu tallafin karatu.

Shugaban karamar hukumar, Aliyu Wakili-Boya shi ne ya bayyana hakan a lokacin bikin dankwa daliban tallafin kudi lakadan, a yankin karamar hukumar.

Mista Aliyu Boya, ya zamu wakilcin Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta Boya Sa’idu Sali, inda daliban da ke yin karatun diploma suka rabauta da samun naira 10,000, a yayin da masu yin karatu a matakin digir suka rabauta da samun Naira 20,000 kowannensu.

Da yake magana a lokacin bikin bayarda tallafin, uban kasar yankin Fufore, Abubakar Mahmoud ya yabawa kokarin Shugaban karamar hukumar na tallafawa harkar ilimi a yankin, inda yayi kira da sauran Shugabannin kananan hukumomi su yi koyi da shi.

Ko a baya ma dai DALIY NIGERIAN ta ruwaito wannan Shugaban karamar hukumar ya kaddamar da aikin fida ga marasa lafiya kyauta a yankin.

LEAVE A REPLY