Hukumomi a babban Birnin tarayya Abuja sun Hana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kaddamar da takararsa ta Shugaban kasa a babban filin taro na Eagles Square dake Abuja babban birnin tarayya.

Tuni dai sanarwa ta fita cewar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai yi bikin kaddamar da takarar sa ta Neman zama Shugaban Kasa a ranar Laraba a Abuja.

Sai dai hukumomi a birnin tarayya sunce hakan ba zata yuwu ba saboda ranar aiki ce, taron zai kawo cikas a Sakatariyar Gwamnatin tarayya dake daura da filin taron na Eagles Square.

Haka kuma an gana Kwankwaso yin makamancin wannan taron a filin taro na Old Parade ground dake babban birnin tarayyar.

LEAVE A REPLY