Marigayi Abdullahi Abubakar Dean

A madadin hukumar gudanarwa ta Jaridar Daily Nigerian Hausa , muna mika sakon ta’aziyar daya daga cikin masu bibiyar shafin wannan jarida Abdullahi Abubakar Dean, wanda ya rasu yau Juma’a bayan wata gajeruwar rashin lafiya.

Abdullahi Abubakar Dean, ya kasance daya daga cikin masu bibiyar wannan jaridar a ko da yaushe. Kafin rasuwarsa ya kasance Malami a jami’ar Bayero dake Kano. Muna fatan Allah ya jikansa ya gafarta masa ya baiwa ‘yan uwansa hakurin rashinsa.

Edita

Daily Nigerian Hausa

LEAVE A REPLY