Shugaban majalisar Sarakunan Gargajiya na jihar Enugu, Igwe Lawrence Agubuzu, yace majalisar taci nasarar dakile al’adar nan ta yiwa yara mata kaciya.

Acewarsa, Sarakunan jihar ne suka hada kai wajen yin kira ga jama’ar jihar da su kaucewa yin wannan ta’ada ta yiwa yara mata kaciya.

Igwe Lawrence yana bayyana haka ne a bikin ranar yaki da yiwa mata kaciya ta duniya da aka gudanar jiya a jihar.

Sarkin yace,akwai rashin tausayi a dinga yankewa yara mata fatar gabansu da kayan da ko tsabta ba su da shi, da sunan al’adar gargajiya, a cewarsa wannan lokacin ya wuce da za’a bar mutane suna cutar da yaransu da sunan kaciya.

Mista Agbuzu wanda ya taba zama jakadan musamman na Majalisar dinkin duniya a kasar Zambiya, kuma tsohon ma’aikacin Diflomasiyya, ya bayyana cewar mata suna da ‘yancinsu da ya kamata a kare musu ta hanyar hana azabtar da su da sunan kaciyar mata.

LEAVE A REPLY