Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewar, an samu yaduwar hotunan bidiyo da suke nuna kananan yara wadan da basu kai lokacin zabe ba, suna jefa kuri’ah a zaben kananan hukumomin da aka yi a jihar Kano kwanan baya.

Shafuka sada zumunta na intanet sun cika da hotunan bidiyon zaben da aka yi a Kano, inda akai ta ganin yadda akai almundahana da rashin gaskiya a zaben, ko dai ta hanyar baiwa wasu kuri’u su dangwale su, ko kuma baiwa kananan yara kuri’ah suna jefawa.

Tuni dai hukumar zabe ta kasa INEC ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki wadannan zarge zarge da akai kan zaben kananan hukumomin jihar kano din. Tunda farko dai, hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewar ba tada laifi kan abinda ya faru a Kano na baiwa yara damar yin zabe.

Shugaban hukumar zaben ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana a Abuja ranar Juma’a cewar, tuni aka kafa kwamitin da zai binciki zaben na jihar Kano, kuma kwamtin zai fara aikinsa a ne sati mai zuwa.

Jama’a d dama ne dai suke ta yin  ta cece kuce kan zaben na jihar kano. Hukumar zabe ta kasa dai tayi amai ta lashe, domin a baya ba kaifinta kan abinda ya faru a kanon, amma yanzu tace da yuwuwar a soke zaben matukar kwamitin da aka kafa ya tabbatar da zarge zargen da aka yi a shafukan sada zumunta na intanet.

Bayan haka kuma, Shugaban jam’iyyar NRM na kasa NIyi Dada a taron da yayi da manema labarai a ABuja, yayi kira ga hukumar zabe ta jihar Kano KANSIEC da ta soke zaben da aka yi a Kano na ranar Asabar da ta gabata.

Acewarsa, an firgita ‘yan adawa a hanyar fito da makamai aka tsorota masu zabe, wanda hakan yayi sanadiyar rashin fitowar mutane jefa kuri’ah. Dada ya bayyana zaben da cewar “Babban koma baya ne” a tarihin zabe a kasarnan.

 

LEAVE A REPLY