Jakadan kasar Burtaniya dake Najeriya ya bayyana goyon bayan kasar Burtaniya ga hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa da EFCC ke jagoranta a Najeriya.

Jakadan ya bayyana haka ne a shafin ofishin jakadancinsu a s Twitter, inda yace kasar Burtaniya na tare da Najeriya na kuma tare da hukumar EFCC wajen yakar cin hanci da rashawa a Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da sabon ginin sakatariyar hukumar a babban birnin tarayya Abuja, taron wanda ya samu halartar tsohon SHugaban kasar Afurka ta kudu Mista Thabo Mbeki da sakataren kungiyar kasashen da Ingila ta yiwa mulkin mallaka da kuma Gwamnan babban Bankin Najeriya.

LEAVE A REPLY