Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki yayi kira ga kwamitin dake kula da shanin matasa da wasannan na majalisar dattawa da ya binciki yadda aka yi ‘yan sanda suka kashe wata mai yiwa kasa hidima a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na facebook ranar Alhamisa da yamma. Bukola Saraki ya kara da cewar “Dukkan wani dan Najeriya rayuwarsa tana da matukar muhimmanci kwarai, musamman matasa wadan suka kawo karfi don fuskantar kalubalan raywa”

Daga karshe Shugaban majalisar yayi adduah ga mai yiwa kasa hidimar da ala lashe sannan kuma ya yiwa iyayanta ta’aziyar rashin da suka yi.

LEAVE A REPLY