Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake gaisawa da Gwamnan jihar Bauchi MA Abubakar yayin da Gwamnan ya kai masa ziyara ofishinsa a kwanakin baya

Sshugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Bauchi a gobe Alhamis. Ana sa ran Shugaba Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka da Gwamnan jihar Mohammed Abdullahi Abubakar ya aiwatar a jihar.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta habarto cewar, wannan shi ne karon farko da Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Bauchi tun bayan zama Shugaban kasa a shekarar 2015.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Umar Sade, shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Talata a Bauchi. Yace ana sa ran Shugaba Buhari zai kawo ziyara jihar ta Bauchi domin kaddamar da aikin hanyoyi da Gwamnan jihar MA Abubakar ya gina.

A cewarsa, wasu daga cikin hanyoyin da Shugaban zai kaddamar suna cikin garin Bauchi ne, yayin da wasu da za’a kaddamar suke a yankin Katagum (Azare da Misau) a jihar Bauchi.

Haka kuma, ana sa ran SHugaban zai kaddamar da rabon taraktar noma guda 500 da Gwamnatin jihar ta samar domin rabawa manoman jihar.

Kwamishinan ya kara da cewar, dukkwan wadan da zasu ci gajiyar wadannan motoci na noma zasu biya kashi 10 daga cikin ainihin kudin da aka sayi motar wato Naira miliyan 15 kowacce daya.

LEAVE A REPLY