Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Hadaddiyar kungiyar kabilar Yarbawa ta Afenifere ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya dauki shawarar da tsofaffin shugabannin kasar nan biyu, Olusegun Obasanjo OBJ da Ibrahim Badamasi Babangida IBB, suka bashi na kar ya tsaya takarar tazarce a shekarar zabe ta 2019.

A jiya Lahadi ne IBB ya fitar da wata sanarwa ta bakin hadiminsa kan harkokin yada labarai, inda ya nemi Shugaba Buhari da ya manta da batun sake tsayawa takara ya bar wa matasa masu sabon jini da sabon tunani.

Ko a makonnin da suka wuce ma (a ranar 23 ga watan Janairu, 2019) sai da tsohon shugaba OBJ ya fitar da wata budaddiyar wasika inda ya bayyana inda bangarorin da Buhari ya gaza tare da bashi shawarar ya hakura da mulki a 2019 ya koma ya zama uban kasa.

Mista Yinka Odunmakin, wanda shi ne mai magana da yawun Afenifere ya ce “Hakika tsofafin shugabannin biyu (OBJ da IBB) sun yi nazari da hange da zai amfani Nijeriya kan batun turbar da jam’iyya mai mulki ta APC a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta jefa al’ummar Nijeriya a ciki.”

A bayanin da Mista Odunmakin ya yi da jaridar Tribune ta wayar salula, kakakin na kabilar Yarbawa ya ce, “Takardun IBB da OBJ na nuna cewa tsofaffin shugabannin biyu na biye da yadda al’amura ke tafiya a Nijeriya kuma tsoma bakinsu akan makomar Nijeriya a shekarar 2019 da bayanta, wata zaburarwa ce ga ‘yan Nijeriya.

“A saboda haka wadanda suke da kunnuwa su saurara su ji zancen iyayen kasa, haka kuma shi ma Buhari ya saurari shawarar da aka bashi don tsira da mutuncinsa. In kuma ya ki, to, al’ummar Nijeriya za su yanke hukunci a shekarar 2019.”

Odunmakin, ya ci gaba da bayyana takaicinsa kan yadda wasu makusanta Shugaba Buhari suka dage kan dole sai ya zarce, inda har suka fara yin kanfen din tazarcen Buhari a shekarar 2019 ba tare da yin duba da halin da Buhari jefa kasar nan a ciki ba.

“Abin mamakin ma shi ne yadda kungiyar Miyetti Allah ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin Buhari ya zarce a sheakar 2019. Me hakan ke nufi? Ganin halin da kasar nan ta fada na halin rashin tsaro da fargaba, duk mutumin da ya nuna cewa ya amince Buhari ya zarc, to, lalle yana da wata ajandar tasa ta kashin kai,” inji Mista Odunmakin.

LEAVE A REPLY