Mai magana da yawun fadar Shugaban kasa Malam Garba Shehu ya bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Rotimi Amaechi a matsayin daraktan yakin neman zabensa na shekarar 2019.

Garba Shehu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a shafinsa na Facebook. Inda ya bayyana cewar Amaechi shi je ya jagoranci zaben da akai nasararsa a shekarar 2015.

LEAVE A REPLY